Isa ga babban shafi
Najeriya

Bamu da karfin kara yawan mafi karancin albashi - Gwamnoni

Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun nanata cewa basu da karfin tattalin arzikin biyan sabon tsarin mafi karancin albashi da kungiyar kwadagon kasar ke nema.

Wasu daga cikin 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriya, yayin gudanar da wata zanga-zanga a birnin Legas. (20/06/2007)
Wasu daga cikin 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriya, yayin gudanar da wata zanga-zanga a birnin Legas. (20/06/2007) REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, kuma gwamnan jihar Zamfara Abdul Aziz Yari ne ya bayyana matsayar tasu, sa’o’i bayan taron da suka yi a Abuja ranar Larabar da ta gabata, wanda suka gayyaci shugaban kungiyar kwadagon Najeriya Ayuba Wabba.

Shugaban kungiyar gwamnonin Abdul Aziz Yari, yace dukkaninsu suna goyon bayan kara yawan mafi karancin albashin ma’aikata a kasar, sai dai matsalar ita ce basu da isassun kudaden tabbatar da muradin.

Sai dai yayin taron da suka yi, gwamnonin sun cimma matsayar soma shirin tabbatar da cewa kowannensu ya biya ma’aikatan dake jiharsa bashin da suke bi.

A lokacin da yake mayarda martani kan matsayar kungiyar gwamnonin, shugaban kungiyar kwadagon Najeriya, Ayuba Wabba, ya ce har yanzu suna kan bakansu dangane da neman karin mafi karancin albashin la’akari da halin kuncin da ma’aikata musamman kanana ke ciki.

Wabba ya kara da cewa, kamata yayi ace tun a shekarar 2016, gwamnatin Najeriya ta kara yawan kudaden mafi karancin albashin da ake baiwa ma’aikata.

Dangane da wannan lamari ne Sashin Hausa na RFI ya tuntubi sakataren hadaddiyar kungiyar kwadagon na Najeriya, Kwamared Nasir Kabir, wanda ya sa kafa ya shure uzurin gwamnonin, tare da yin kira ga wadanda ba za su iya biyan karin mafi karancin albashin ba da su yi murabus daga mukamansu.

01:01

Kwamared Nasir Kabir kan batun karin mafi karancin albashin ma'aikata a Najeriya

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.