rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Kaduna Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za mu hukunta masu hannu a rikicin Kaduna- Buhari

media
Shugaba Muhammadu Buhari tare da shugabannin al'ummar jihar Kaduna Aminu Sado

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce, gwamnatinsa za ta dauki matakai masu tsauri wajen hukunta wadanda ke da hannu a kisan jama’a a jihar Kaduna.


A yayin ziyarar da ya kai jihar, shugaba Buhari ya bayyana bacin ransa game da asarar rayukan al’umma a rikicin da ya barke a Kasuwar Magani da wasu sassan jihar.

Kimanin mutane 55 ne suka gamu da ajalinsu a rikicin mai nasaba da kabilanci da addini a Kaduna.

A yayin zantawa da shugabannin addini da sarakunan gargajiya da 'yan siyasa da shugabannin al’umma har ma da jami’an tsaro, shugaba Buhari  ya ce, “Idan a can baya, ‘masu kisan’ sun kauce wa fuskantar hukunci, to a yanzu za mu hukunta masu hannu a kisan baya-bayan nan”

Latsa alamar sautin da ke kasa don sauraren rahoto kan ziyarar Buhari a Kaduna.

Rahoto kan ziyarar shugaba Buhari a Kaduna 30/10/2018 Saurare

Wasu na caccakar gwamnatin Buhari kan yadda take gazawa wajen tunkarar tashe-tashen hankulan da suka lakume dubban rayukan jama’a.

Koda yake a wannan karo, shugaban ya jaddada matsayinsa na daukar tsauraran matakai kan masu haddasa rikice-rikicen.

Shugaba Buhari ya kuma jajanta wa al’ummar jihar Kaduna game da asarar da wannan rikici ya janyo musu.