rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Kano

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ganduje ya gaza bayyana a gaban kwamitin majalisa

media
Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Premium Times

Kwamitin mjalisar dokokin Kano dake gudanar da binciken faifan bidiyon da ya nuna gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje na karbar na goro daga wajen wasu ‘yan kwangila, yayi zama karo na biyu.


To sai dai kuma Gwamna Ganduje da aka tsara zai zo gaban kwamitin a wannan zama don kare kan sa, ya gaza baiyyana, inda ya tura da wakilci.

Kwamishinan yada labaran jihar Kano Kwamred Muhammad Garba ne ya wakilci gwamnan, a gaban kwamitin mai manbobi guda bakwai.

Cikin wata wasika da Ganduje ya aikewa kwamitin, gwamnan ya bayyana faifan bidiyon da aka fitar akansa da cewa yunkuri ne kawai na bata masa suna, yayinda ake tunkarar zabukan 2019, inda ya nemi jama’a da su yi watsi da shi.

Yayinda zantawa da manema labarai bayan kammala zaman na yau, shugaban kwamitin binciken Baffa Babba Dan Agundi ya ce rashin bayyanar gwamnan jihar ta Kano ba zai shafi sahihancin binciken da za su yi ba.

Tun da fari dai kwamitin ya baiwa gwamnan zabin bayyana da kansa ko kuma ya tura wakilci.

Daga jihar Kano wakilinmu Abubakar Isah Dandago ya aiko mana da rahoto.

Ganduje ya gaza bayyana a gaban kwamitin majalisa 02/11/2018 - Daga Abubakar Issa Dandago Saurare