rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Muhammadu Buhari Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun Ma'aikatu ta hana NLC da TUC tsunduma Yajin aiki a Najeriya

media
Shugaban kungiyar kodago ta Najeriya Ayuba Philibus Wabba rfi

Kotun sasanta rigingimun Ma'aikata a Nigeria ta hana kungiyar Kodago ta kasar shiga yajin aiki da ta sanar za ta fara daga ranar Talata saboda neman abiya ma aikata albashin mafi karanci na kudi Naira Dubu 60.


Kotun sasanta rigingimun kodagon karkashin mai sharia Sanusi Kado ta bayar da umarnin sakamakon bukatar da Gwamnatin kasar ta gabatar don a hana yajin aikin.

Kotun tace daukan matakin hana yajin aikin ya zama dole saboda muhimmancin batun da aka gabata mata.

Kotun ta tsaida ranar takwas ga wata, wato Alhamis domin sauraron karar sosai.