rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Ilimi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Malaman Jami'o'in Najeriya sun fara yajin aiki

media
Tambarin Kungiyar ASUU a Najeriya The Herald Nigeria

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta fara yajin aikin sai-baba-ta-gani a ranar Litinin bayan gwamnatin kasar ta gaza biya mata bukatunta.


ASUU ta sanar da daukar matakin ne na tsunduma cikin yajin aikin jim kadan da kammala taron Majalisr Kolinta a birnin Akure na jihar Ondo a cikin daren da ya gabata.

Kungiyar ta zargi gwamnatin da gaza aiwatar da yarjejeniyar da suka rattabawa hannu, in da ta jaddada cewa, yajin aikin zai shafi daukacin jami’o’in gwamnatin tarraya da na jihohi.

Shugaban ASUU, Farfesa, Biodun Ogunyemi ya ce, za su ci gaba da yajin aikin har sai gwamnatin kasar ta cika alkawuran da ta yi musu.

Farfesa Ogunyemi ya kuma zargi gwamnatin da nuna rashin kulawa ga jami’o’in kasar saboda a cewarsa, ‘ya’yan manyan ‘yan siyasa da masu hannu da shuni na karatu ne a jami’o’i masu zaman kansu.