rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari zai tura kudurin neman karin albashi zuwa majalisa

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Darren Ornitz/File Photo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi rahoton tattaunawar da masu ruwa da tsaki a kasar suka yi, kan bukatar kungiyar kwadago ta neman karin mafi karancin albashin ma’aikata daga naira dubu 18,000 zuwa naira 30,000.


Buhari ya karbi rahoton ne a Abuja, daga kwamitin da gwamnati ta kafa, da aka dorawa alhakin duba yiwuwar karin mafi karancin albashin, wanda ya kunshi wakilai daga bangaren gwamnati, kungiyar kwadago da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Shugaban Najeriyar ya kuma yi alkawarin aikewa da kudurin karin albashin zuwa majalisun tarayyar kasar, domin tabbatar da shi a matsayin doka.

A makon da ya gabata ne kungiyar kwadagon Najeriya ta sha alwashin shiga yajin aikin gama gari a wannan Talata 6 ga watan Nuwamba, 2018, muddin gwamnati ta gaza amincewa da bukatar karin albashin.

Sai dai a ranar Litinin kungiyar kwadagon Najeriyar ta janye aniyar shiga yajin aikin, bayan ganawar da wakilanta suka yi da bangaren gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.