rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotu ta umarci a tsare mutane 19 kan zargin kashe Janar Alkali

media
Marigayi Manjo Janar Idris Alkali mi ritaya Saharacable

Wata kotu a Jihar Filato da ke Najeriya ta bada umurnin tsare mutane 19 da ake zargi da hannu wajen kisan gillar da aka yi wa Janar Idris Alkali mai ritaya a karamar hukumar Jos ta Kudu.


Mai Gabatar da kara Emmanuel Ochoba ya ce, ana tuhumar mutanen ne da hada baki kan kitsa kisan da kuma aiwatar da shi, in da ya bukaci alkali Danjuma Longji ya bada umurnin tsare wadanda ake zargin a gidan yari har sai sun kammala binciken su.

Lauyan wadanda ake kara, Gyang Zi ya bayyana cewar mutane 19 sun ki amincewa da tuhumar da ake musu, kuma daga bisani Mai Shari’a Longji ya dage sauraron karar zuwa 10 ga watan Disamba mai zuwa.

Tuni aka gudanar da jana'izar marigayin bayan gano gawarsa a cikin wata tsohuwar rijiya a makon jiya.