rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

NLC ta janye yajin aikin gama-gari a Najeriya

media
Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya Ayuba Philibus Wabba tare da mambobin kungiyar REUTERS/Afolabi Sotunde

Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC ta janye yajin aikin gama-garin da ta shirya gudanarwa a ranar Talata don tilasta wa gwamnatin kasar amincewa da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikata.


Shugaban NLC, Ayuba Wabba ya shaida wa manema labarai cewa, sun janye yajin aikin ne bayan cimma matsaya da bangaren gwamnati kan wannan batu a wata ganawa da suka yi a cikin daren da ya gabata a birnin Abuja.

Wabba ya ce, sun rattaba hannu kan wasu takardu kuma da yammacin ranar Talata za a gabatar da rahoton cimma matsayar ga shugaba Muhammadu Buhari.

Ko da yake shugaban na NLC, bai yi cikakken bayani ba game da ainihin albashin da gwamnatin ta ce, za ta iya biyan ma’aikatan, in da ya ce, za a bayyana adadin kudin ga jama’a bayan gabatar da rahoton ga shugaba Buhari.

Kungiyar Kwadagon ta shafe tsawon shekaru na fafutukar ganin gwamnatin kasar ta amince da bukatarta ta mafi karancin albashin ma’aikata, in da ta ce, ba za ta amince da Naira dubu 18 ba a yanzu.