rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Ingila Muhalli

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yarima Charles zai taimaka wajen sulhunta rikicin manoma da makiyaya

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin karbar bakuncin Yarima Charles tare da matarsa Camilla. RFIHAUSA

Shugaban Kungiyar kasashe renon Ingila, kuma mai jiran gadon sarautar Ingila, Yarima Charles, ya fara ziyarar aiki a Najeriya.


Ana sa ran yayin ziyarar tasa, Yarima Charles zai gana da hukumomin kasar, da kuma shiga tsakani kan yadda za’a magance rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Ziyarar ta Yarima Charles da matarsa Camilla zuwa Najeriya, bangare ne daga cikin rangadin tsawon mako guda zuwa wasu kasashen nahiyar Afrika.

Muhammad Kabir Yusuf na dauke da karain bayani a wannan rahoto.

Yarima Charles zai sulhunta rikicin manoma da makiyaya 06/11/2018 - Daga Kabir Yusuf Saurare