rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Gwamnati na ciyar da Az-zakzaky abincin Naira miliyan 3 a duk wata"

media
Shugaban Mabiya Akidar Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky Tasnimnews

Gwamnatin Najeriya na kashe kimanin Naira miliyan 3.5 a kowanne wata wajen ciyar da shugaban mabiya akidar Shi’a da ke tsare shekaru biyu, Sheik Ibrahim Az-zakzaky.


Ministan Yada Labarai na Kasar, Lai Mohammed ya bayyana haka a wani faifen bidiyo da ake yadawa a kasar a dai lokacin da wata kotu a jihar Kaduna ta ki amince wa da bayar da belin Az-zakzaky.

Koda dai a cikin bidiyon, an jiyo Ministan na gargadin ‘yan jarida da nadan muryarsa a yayin bayar da jawabin, amma duk da haka sai da bidiyon ya yadu.

Tuni faifen bidiyon ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta, in da wasu ke caccakar Ministan kan wadannan kalamai.

Tun a cikin watan Disamban 2015 ake tsare da Az-zakzaky bayan sojoji sun kashe magoya bayansa akalla 347 a wata tarzoma da ta kaure a garin Zaria.

Sojojin sun zargi mabiya Shi’ar da hana tawagarsu da ke da shugabansu, Tukur Buratai wucewa.

Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama na ciki da wajen Najeriya sun yi Allah-wadai da kisan da sojin suka yi wa ‘Yan Shi’ar a wancan lokaci, kuma a yanzu haka Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya na gudanar da bincike kan lamarin.