rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Najeriya Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya za ta gudanar da sahihin zabe a 2019 - Amurka

media
Tibor Nagy, Mataimakin Sakataren Jakadan Amurka dake lura da harkokin nahiyar Afrika. The East African

Amurka tace tana da karfin gwiwar Najeriya za ta gudanar da sahihin zabe a shekarar 2019.


Mataimakin Sakataren Jakadan Amurka dake lura da harkokin nahiyar Afrika, Tibor Nagy ne ya bayyana haka, yayin wata ziyara da ya kawo Najeriya a baya bayan nan.

Nagy ya ce aikin dake gaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC gagarumi, sai dai duk da haka, suna da kwarin gwiwar shugaban hukumar Farfesa Yakubu sai sauke nauyin da ya rataya a wuyansa yayin zabukan na 2019 dake tafe.

A cewar jakadan na Amurka, tuni Najeriya ta zama abin kyakkyawan koyi musamman a fagen zabe na dimokaradiyya a nahiyar Afrika, idan aka yi la’akari da yadda hukumar zaben kasar INEC ta gudanar da zabukan shekara ta 2015.

Yayin ziyarar tasa, Tibor Nagy ya jaddada cewa Amurka ba ta goyon bayan kowane dan takarar zaben shugabancin kasar a zaben 2019 dake tafe.