rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Noma

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya ta rage shigo da abinci da kashi 60

media
Gwamnatin Najeriya ta rage shigo da shinkafa da wasu nau'ukan abinci da kashi 60 cikin 100 tun daga shekarar 2015 post-nigeria.com

Gwamnatin Najeriya ta rage shigo da abinci daga kasashen ketare da akalla kashi 60 cikin 100 tun daga shekarar 2015 zuwa yanzu.


Shugaban Babban Bankin Kasar, Godwin Emefiele ya bayyana haka a wani taron da aka gudanar a Jihar Jigawa da ke arewacin kasar, in da ya ce, matakin ya bai wa gwamnti damar ajiyar Dala miliyan 800.

Na’ukan abincin da aka rage shigo da su sun hada da shinkafa da alkama da siga da tumatur da kuma madara.

Shugaban Bankin ya ce, ya zuwa shekarar 2013, an kashe Dala biliyan 1.4 wajen shigo da wadannan na’u’ukan abincin biyar, sabanin Dala miliyan 678.6 da aka kashe ya zuwa karshen shekarar bara.

Emefile ya ce, bankin CBN na tallafa wa wani shirin noman shinkafa domin karfafa gwiwar masu hada-hadarta musamman a karkara.