rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Najeriya Gasar Cin Kofin Afrika Afrika ta kudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wasan Super Eagles da Afrika ta kudu ba mai sauki ba ne - Rohr

media
Rohr ya ce duk da karancin ‘yan wasan da ya ke fuskanta yana fatan tawagar ta Super Eagles ta fitar da kasar kunya wajen samun damar shiga gasar ta cin kofin Afrika. AFP PHOTO/Ian KINGTON

Kociyan kungiyar kwallon kafar Super Eagles da ke Najeriya Gernot Rohr ya ce wasansu da Bapana Bapana ta Afrika ta kudu zai zamo mafi wahala ga bangaorin biyu musamman ganin yadda ita Super Egles za ta yi wasan na gobe Asabar ba tare da wasu ‘yan wasanta ba.


A cewar Rohr yanzu haka ‘yan wasa irinsu mai tsaron baya na Najeriyar Shehu Abdulahi, da mai tsaron raga Francis Uzoho da kuma dan wasan gaba Odion Ighalo na fama da rashin lafiyar da baza su samu damar taka leda a wasan ba, yayinda dan wasan tsakiya da ke taka leda a Leicester City Wilfred Ndidi ke fuskantar dakatarwa.

Shekara guda kenan dai cikin watan Yuni da Najeriyar da buga wasa da Afrika ta kudu har gida a jihar Uyo ta kuma sha kaye da ci 2 da banza.

Sai dai Rohr ya ce duk da karancin ‘yan wasan da ya ke fuskanta yana fatan tawagar ta Super Eagles ta fitar da kasar kunya wajen samun damar shiga gasar ta cin kofin Afrika.

Yanzu haka dai Super Eagles wadda ta taba lashe kofin Afrikan har sau uku kuma ta ke matsayin jagora a rukuninta na E da maki 9 ta isa Johannesburg na Afrika ta kudu don fara shirye-siryen wasan na gobe da zai gudana da karfe 3 na rana.