rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kano Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Fadar Kano za ta nadawa Naziru Ahmad Sarautar Sarkin Mawaka

media
Naziru Ahmad shahararren mawakin Hausa. YouTube

Fadar mai martaba sarkin Kano dake Najeriya, ta sanar da nada shahararen mawaki Nazir Ahmad a matsayin Sarkin Mawakan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na biyu.


Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma'aikatan Fadar Kanon Munir Sunusi, tace lura da gudummowar daya baiwa Sarkin Kano tun yana matsayin Dan Majen Kano, da kuma zamowarsa Sarki, yasa ya fadar girmama shi da wannan sarauta ta Sarkin mawaka.

Shi dai mawaki Nazir Ahmad ya shahara ta fuskar wakokin Sarakuna da fitattun attajirai a arewacin Najeriya amma da salon zamani, zalika yayi wasu wakokin da suka fita a fina-finan hausa

An tsaida 27 ga Watan Disamba a matsayin ranar da za'ayi bikin nadin sarautar a fadar Masarautar Kano.