rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Ni ne hakikanin Buharin da aka sani ba Jibril daga Sudan ba"

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Audu MARTE / AFP

A karon farko, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya maida martani kan jita-jitar da wasu ke yadawa kan cewa ba shi ne hakikanin Buharin da aka sani ba.


Shugaba Buhari ya karyata bayanan dake cewa wai shi wani mutum ne mai suna Jibrin daga kasar Sudan, da aka yiwa gyaran kamanni, kuma aka turo domin ya ci gaba da mulkin Najeriya bayan rasuwar Buhari na asali da yayi rashin lafiya.

Shugaban ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da 'yan Najeriya mazauna kasar Poland.

A cewar Buhari, mutane da dama sun yi burin ganin mutuwarsa a lokacin da ya kwanta rashin lafiya mai tsanani, wadanda suka rika yin kamun kafar nema zama mataimakan Farfesa Yemi Osinbajo idan rai yayi halinsa.

An dai shafe tsawon lokaci, jagoran kungiyar IPOB Nnamdi Kanu da ya tsare daga Najeriya, yana ikirarin cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ba shi ne hakikanin Buharin da aka sani ba.