rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika Bankin duniya Hakkin Mata Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Afrika na tafka hasarar biliyoyin kudi saboda yiwa mata auren wuri

media
Kididdiga ta nuna cewa kasashen nahiyar Afrika 12 na tafka hasarar dala biliyan 63 da ya kamata su samu daga manyan kasashe ta fannin bunkasa ilimin yara mata, a dalilin yi musu auren wuri. AFP

Bankin Duniya yace sama da kashi daya bisa uku na ‘Yam mata a Yankin Afirka dake kudu da Sahara na afkawa cikin aure tun kafin su cika shekaru 18, abinda yake sanya wadannan kasashe tafka asarar biliyoyin daloli na kudaden da ya dace su samu.


Rahotan bankin yace kasashe 12 da matsalar ta shafa na asarar Dala biliyan 63 saboda rashin kammala karatun ‘Yam matan, sabanin wadanda ke aure bayan sun haura shekaru 18.

Rahotan da aka yiwa lakabi da ‘Educating Girls and Ending Child Marriage’ yace kowacce shekara ana samun raguwar yaran dake kammala karatun sakandare domin fadawa aure da kashi 5 ko kuma sama da haka.

Bankin yace matsalar tafi kamari a kasashen Afirka ta Yamma inda ake samun karuwar ‘Yam matan dake aure tun kafin su cika shekaru 15, kuma daga cikin kasashe 20 da aka fi samun matsalar 18 na Afirka ne.

Binciken da bankin ya gudanar ya danganta matsalar auran da ‘Yam matan da al’ada da sauyin yanayi da rikice rikice da kuma talauci.