rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia
  • Yau ake zama a bainin jama'a game da tsige Shugaban Amurka Trump
  • Wasu 'yan kasar Kamaru sun shiga Otel da Shugaba Paul Biya ke ciki a Paris.
  • Tashin Bam a Kabul na Afghanistan ya kashe mutane 7
  • Saudiya, Daular Larabawa da Bahrain za su shiga wasannin kwallon kafa tare
  • Hari daga Israila ya kashe Bafalastine daya
  • Amurka ta gargadi 'yan kasar daga zuwa Bolivia

Najeriya Qatar Rashawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An bai wa Nuhu Ribadu lambar girma kan yakar rashawa a Najeriya

media
Tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu yayin karrama shi da lambar girma kan rawar da ya taka wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar. RFI hausa

An gudanar da wani bikin karrama mutanen da suka ba da gudunmawa wajen yaki da cin hanci da rashawa a sassa daban-daban na duniya. Bikin wanda ya gudana yau Juma'a a kasar Qatar ya yaba da irin gudunmawar da daidaikun mutane ke bayarwa wajen fatattakar ayyukan cin hanci da Rashawa cikin al'umma.


Kyautar wadda aka kasa ta a matakai daban daban ta duba irin gudumawar da jamiā€™ai ke bayarwa wajen dakile yaduwar cin hanci da ke yi wa hukumomi illa da kuma tabbatar da hukunta wadanda suka aikata laifin.

Malam Nuhu Ribadu, tsohon shugaban Hukumar EFCC da ke Najeriya na daya daga cikin wadanda aka bai wa lambar girma na nuna gwarzantaka wajen yaki da cin hancin saboda rawar da ya taka a baya.

Bikin ya gudana a karkashin Sarkin Qatar, Sheikh Tamim Bin Hammad al Thani da Firaministan Malaysia Mahathir Mohammed da kuma Babban Daraktan ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da safara kwayoyi Mr Yuri Fedoyov.

Lambar girmar na dauke da tukucin Dala 250,000.