Isa ga babban shafi
Najeriya

Malaman Kwalejojin Ilimi da na Kimiya sun soma yajin aiki

Malaman makarantun kwalejojin ilimi da na kimiya da fasaha a Najeriya sun tsunduma cikin yajin aikin gama gari.

Wasu malaman makarantun kwalejojin ilimi da na kimiya da fasaha a Najeriya.
Wasu malaman makarantun kwalejojin ilimi da na kimiya da fasaha a Najeriya. Premium Times Nigeria
Talla

Malaman sun dauki matakin ne, saboda abinda suka kira rashin aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin kasar a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2017.

Shugaban malaman kwalejojin fasahar Usman Dutse ya shaidawa manema labarai cewa, gwamnati ta gayyace su domin tattaunawa ranar 17 ga watan nan, amma hakan ba zai sanya su janye yajin aikin ba.

Yayinda yake yiwa sashin Hausa na RFI karin bayani, Abdullahi Yelwa daya daga cikin malaman, ya ce daga cikin dalilan da suka tilasta shiga yajin aikin n agama gari akwai, rashin aiwatar da rahoton kwamitin da gwamnati ta kafa a 2014, wanda ya zagaya kwalejojin ilimin da na kimiya da fasaha domin tantance bukatunsu ga gwamnati.

Sai kuma wasu gwamnatocin jihohi da har yanzu basu biya malaman makarantun albashi na tsawon watanni 14 ba.

A cewar Yelwa jihohin sun kunshi, Abia, Edo, Kogi, Imo, Osun, Ogun, Ondo, Benue da kuam Oyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.