Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun hallaka jami'an tsaro 14

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar mutuwar sojojinta 13 tare da jami’in dan sanda daya a hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai musu a jihar Yobe.

Wasu sojin Najeriya yayin sintiri a garin Maiduguri, jihar Borno.
Wasu sojin Najeriya yayin sintiri a garin Maiduguri, jihar Borno. REUTERS/Stringer
Talla

Kanal Onyema Nwachukwu, wanda ya yi magana da yawun rundunar sojin, ya ce a ranar Litinin mayakan Boko Haram sun kaiwa sansanin dakarunsu farmaki da ke Kukareta a Damaturu da misalin karfe 6 na yammaci.

Sai dai sojin Najeriyar sun maida martani, inda suka yi nasarar hallaka mayakan na Boko Haram da dama, wadanda kawo yanzu ba’a bayyana adadinsu ba, sai kuma soja daya daya jikkata.

Sanawar da Kanal Nwachukwu ya fitar, ta kara da cewa mayakan na Boko Haram sun kuma kai wani farmakin na daban, inda suka yiwa wasu sojojin runduna ta daya, da ke kan aikin rakiyar motoci kwanton bauna a tsakanin hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, inda a nan ne aka rasa sojoji 13 da jami’in dan sanda daya.

Kanal Nwachukwu ya ce a halin yanzu, dakarun soji suna ci gaba da farautar mayakan na Boko Haram da suka kai hare-haren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.