Isa ga babban shafi
Najeriya

Na cika alkawuran da na yi a zaben 2015- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, ya cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabensa a shekarar 2015 duk da shakkun da ‘yan adawa ke nunawa .

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Reuters
Talla

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da yakin neman sake zaben sa a shekakar 2019, karkashin inuwar jam’iyyar APC a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a ranar Juma’a.

A cewar Buhari, al’ummar Najeriya ba za su yi nadamar kada kuri’unsu ga ‘yan takarar jami’yyar APC a zaben 2019 da ke tafe ba.

Shugaban ya ce, ya cika alkawuransa a bangarorin da suka shafi tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa, yayin da ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da sa kafar wando daya da masu wawure dukiyar talakawa muddin ya koma kan karagar mulki.

Koda yake Buharin ya ce, yaki da mayakan Boko Haram na ci gaba da zama kalubale a wasu sassan kasar, amma za a kawar da matsalar tsaron da kungiyar ke haifarwa a kasar.

Har ila yau, Buhari ya ce, matsalar rashin aikin yi na ci gaba da addabar kasar, amma gwamnatin na kokarin shawo kanta.

A bangaren harkar noma kuwa, shugaba Buhari ya ce, gwamnatinsa ta karfafa guiwar manoma don tabbatar da tsaron abinci a fadin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.