Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun fara kwashe jama'ar Baga zuwa tuddan mun tsira

Gwamnatin jihar Borno da hadin guiwar rundunar Sojin Najeriya sun fara wani aikin kwashe mutanen Baga da ke karamar hukumar Kukawa a jihar, zuwa tuddan mun tsira don tseratar da su daga yakin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin sojin Najeriyar da mayakan Boko Haram a yankin.

Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya.
Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya. Reuters
Talla

Cikin sanarwar da ta fitar ta hannun mataimakin kakakinta na rundunar ‘Operation Lafiya Dole’, Kanal Onyema Nwachukwu a ranar Lahadi, rundunar sojin Najeriyar ta ce matakin zai bai wa dakarunta na kasa da na sama, damar luguden wuta kan dukkanin wuraren da mayakan Boko Haram ke amfani da su a matsayin maboya ko sansanoni cikin garin na Baga.

Sanarwar ta kuma ce, matakin kwashe fararen hular bai shafi mazauna garuruwan da suka hada da Bama, Dikwa da kuma Mongunu ba, la’akari da cewa farmakin da dakarun Najeriyar za su kaddamar a Baga ba zai shafe su ba.

Wakilinmu da ke Maiduguri, ya tabbatar mana cewa wani lokaci da yammacin wannan Litinin, ake sa ran samun karin bayani kan shirin na kwashe fararen hular daga Baga, bayan kammala taron majalisar tsaro tsakanin kwamandojin rundunar ‘Operation Lafiya Dole’, sauran hukumomin tsaro da kuma gwamnatin jihar Borno.

A tsakiyar makon da ya gabata ne wasu gungun mayakan Boko Haram suka kai farmaki kan sansanin sojoji da ke Baga, wanda bayan shafe sa’o’i ana fafatawa, dakarun suka janye domin baiwa jiragen yaki damar gaggauta murkushe harin mayakan, sai dai rahotanni na nuni da cewa har yanzu mayakan suna garin.

Wata kididdiga da hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta fitar a baya bayan nan, ta nuna cewa an samu karin mutane dubu 2 da 46 a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Maiduguri, bayan harin da mayakan na Boko Haram suka kaddamar a garin na Baga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.