Jirgin sojin Najeriya ya yi batan-dabo a Borno
Jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar sojin saman Najeriya, ya yi batan-dabo a dai dai lokacin da yake gudanar da aikin taimakawa dakarun bataliya ta 145 da ke yaki da Boko Haram a garin Damasak a jihar Borno.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola ya fitar a cikin daren da ya gabata, ta ce, al’amarin ya faru ne da misalin karfe 7:45.
Sanarwar ta ce, babu cikakken bayani game da musabbabin hatsarin jirgin mai saukar ungulu, amma rundunar ta yi alkawarin karin haske ga jama’a da zaran ta samu cikakken bayani.
Wanann na zuwa ne bayan Daramola ya sanar da nasarar da rundunar Operation Lafiya Dole ta samu game da lalata wani gini da mayakan Boko Haram ke amfani da shi domin gudanar da taro a garin Baga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu