rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zamfara Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kama masu taimakawa 'yan bindigar Zamfara a Legas

media
Wasu Shanu mallakar Fulani makiyaya a jihar Kaduna, da ke arewa maso yammacin Najeriya. STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi nasarar damke wasu mutane 4 da ke sana’ar saida shanu a mayankar dabbobi da ke karamar hukumar Agege a jihar Legas, bisa zargin mutanen suna taimakawa wasu 'yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar Zamfara.


‘Yan sandan sun shaidawa manema labarai cewa, mutanen suna taimakawa ‘yan bindigar ne ta hanyar sayen Shanu da sauran dabbobi na sata da barayin ke satowa daga jihar ta Zamfara, da kuma wasu sassan arewacin Najeriya.

Binciken jami’an tsaron Najeriya ya kuma gano cewar, ‘yan bindigar suna amfani da kudaden shanun satar wajen sayen muggan makamai daga Libya, su kuma yi amfani da su wajen kai farmaki kan garuruwan Tsafe, Zurmi, Shinkafi, Maradun, Maru da Brinin-Magaji da ke jihar ta Zamfara.

Mutane hudun da aka kama a jihar at Legas, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana, sun hada da Alawani Abubakar, Alhaji Ago Atine, Mohammed Shagari da kuma Bashiru Aliyu.