Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kai sabon hari a Rann

Wasu da ake zatan mayakan Boko Haram ne, sun kashe mutane akalla 10 tare da kona gidaje da dama a wani hari da suka kaddamar a garin Rann da ke karamar hukumar Kala-Balge da ke jihar Bornon Najeriya.

Hare-haren Boko Haram sun kazanta a 'yan kwanakin nan
Hare-haren Boko Haram sun kazanta a 'yan kwanakin nan pmnewsnigeria
Talla

Majiyoyi sun rawaito cewa, mutane da dama sun jikkata a farmakin wanda aka kai cikin daren da ya gabata.

Maharan sun isa garin ne cikin ayari, in da kuma suka far wa sansanin soji, yayin da rahotanni ke cewa, an kwashe tsawon sa'o'i ana musayar wuta tsakanin sojin da mayakan.

Majiyoyin sun ce, mayakan sun fatattaki sojojin saboda irin manyan makaman da suke dauke da su.

Hare-haren Boko Haram sun kazanta a ‘yan kwanakin nan, al'amarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji suka janye ma’aikatansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.