Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya kare matakinsa na dakatar da Alkalin Alkalan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kare matakin da ya dauka na dakatar da alkalin alkalan kasar Walter Onnoghen, a dai dai lokacin da 'yan adawa ke sukar matakin da kakkausan harshe.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Dan takarar shugabancin Najeriya na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya bayyana dakatar da mai shari'a Onnoghen a matsayin kama karya, yayin da shugaban majalisar dattijan kasar Bukola Saraki, ya ce matakin na shugaba Muhammadu Buhari, ya sabawa tsarin mulki na dimokaradiyya.

Sai dai, shugaba Buhari, wanda ya rantsar da mai shari’a Ibrahim Tanko, a matsayin mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya, ya ce dakatar da Onnoghen ya biyo bayan umarnin kotun kasar ta da’ar ma’aikata, wadda ta ce za a tantance makomar Onnoghen, bayan kammala shari’arsa ta laifin kin bayyana wasu kadarori da ya mallaka.

Zalika, yayin kare matakin dakatar da tsohon alkalin alkalan, Buhari, ya ce kamata yayi tun da fari, mai shari'a Onnoghen, ya saukakawa kowa wajen sauka daga mukaminsa bisa radin kansa, la’akari da cewa, da hannunsa ya rubuta amincewa da aikata laifin kin bayyana wasu kadarorin nasa, abinda ya daganta da kuskure da kuma mantuwa.

Matakin sauya alkalin alkalan Najeriya dai na ci gaba da zama maudhu’in tafka muhawara tsakanin ‘yan kasar da wasu masana shari’a, inda wasu ke goyon bayan matakin, wasu kuwa na kallonsa a matsayin kuskure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.