Isa ga babban shafi
Najeriya

INEC ta sake jaddada matsayinta kan makomar APC a Zamfara

Hukumar shirya zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta jaddada matsayinta na cewa, jam’iyyar APC ba ta da ‘yan takara a matakan zabukan jihar Zamfara.

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta Farfesa Mahmud Yakubu.
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta Farfesa Mahmud Yakubu. News Express Nigeria
Talla

INEC ta bayyana matsayin nata ne bayan kammala wani taro da ta yi a Larabar nan, wanda bayansa hukumar INEC din ta kara tabbatar da cewa jam’iyyar ta APC ba ta gudanar da karbabben zaben fida gwanayenta ba a matakin jihar ta Zamfara.

Matakin na INEC ya zo ne bayan da wasu manyan kotuna biyu suka yanke hukunce-hukunce masu cin karo da juna kan makomar APC a zabukan jihar Zamfara na 2019.

A ranar Juma’ar makon da ya gabata, babbar kotun Zamfara da ke Gusau, ta yanke hukuncin tabbatar da zaben fidda gwanin Jam’iyyar APC a jihar, wanda ya gudana a ranakun 3 da 7 ga watan Oktoban shekarar 2018.

Kotun wanda ke karkashin mai Shari’a Muhammad Bello Shinkafi, ta kuma umarci hukumar zaben Najeriya INEC, ta amince da zaben fidda gwanin na APC da ya shafi mukamin gwamna, ‘yan majalisun dokokin tarayya da kuma na dokokin jihar.

Sai dai a rana guda kuma, babbar Kotun Najeriya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa hukumar INEC tana da ikon kin karbar 'yan takarar jam'iyyar APC a zabukan na jihar Zamfara.

Yayin gabatar da hukuncin a ranar ta Juma'a 25 ga watan Janairu, mai shari'a Ijeoma Ojukwu, ta ce rashin 'yan takarar APC a Zamfara ba laifin hukumar INEC bane, laifi ne na jam'iyyar kanta, saboda gaza kammala zabukanta cikin wa'adin da aka tsara domin zabukan fidda gwanin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.