Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya kaddamar da aikin neman danyen mai a Bauchi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin neman danyen man fetur a kogin Kolmani da ke gaf da yankin Barambu a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin kaddamar da aikin neman danyen man fetur a kogin Kolmani da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin kaddamar da aikin neman danyen man fetur a kogin Kolmani da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi. Vanguard Nigeria
Talla

Yayin kaddamar da aikin a ranar Juma’a, shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta maida hankali wajen kokarin gano albarkar danyen man a dukkanin yankunan da binciken masana ya nuna cewa, akwai yiwuwar samun rijiyoyin danyen man da kuma iskar gas.

Yankunan da masana suka yi hasashen samun danyen man sun hada da Tafkunan Chadi, Gongola, Sokoto, Dahomey, Tafkin Bida da kuma na Anambra, sai kuma wani yanki a jihar Benue.

Shugaban Najeriyar ya ce tashi haikan domin neman albarkatun danyen man a yankunan da aka lissafa, bangare ne na cika alkawuran da ya dauka na karfafa tattalin arzikin Najeriya, wanda ya ce, albarkatun danyen mai da na iskar gas na da tasiri akansa, a halin yanzu da ma nan gaba.

Shugaban Kamfanin Man Najeriya (NNPC) Mai Kanti Baru, ya ce aikin neman danyen mai a kogin Kolmani ya fara ne tun a shekarun 1990, a lokacin kuma wasu kamfanonin hakar mai na Turai suka gano cewa, akwai sinadarin Hydrocarbon mai yawa a wata rijiya da ke kogin na Kolmani, wanda ke nuna za’a iya samun Iskar gas da yawanta zai iya kaiwa ma’aunin Cubic biliyan 33.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.