Isa ga babban shafi
Najeriya

Yajin aikin malaman jami'o'in Najeriya zai kai makon gobe

Taron da ya gudana tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar malaman jami’o’in kasar ASUU, ya gaza cimma matsayar kawo karshen yajin aikin da malaman suka shafe sama da watanni biyu suna yi.

Wasu daliban Jami'a a Najeriya.
Wasu daliban Jami'a a Najeriya. Premium Times Nigeria
Talla

Yayin zantawa da manema labarai bayan taron na ranar Juma’a, ministan kwadagon Najeriya Chris Ngige ya ce ganawar tasu ta tsawaita, sabanin fatan kammalawa a ranar ta Juma’a, sai dai duk da haka ana gaf da kawo karshen yajin aikin.

Cikin watan Disambar bara, kungiyar malaman jami’o'in ta Najeriya ASUU, ta gindaya sharadin janye yakin aikin da 'ya'yanta suke yi na sama da watanni biyu, inda ta bukaci gwamnatin kasar ta baiwa jami’o’in naira biliyan 50.

Sai dai bayan taron karshen makon nan, ministan kwadago Chris Nigige, ya jaddada cewa gwamnati ba za ta iya mika jimillar kudin a lokaci guda ba.

A halin yanzu an tsayar da 7 ga watan Fabarairu, a matsayin ranar da za’a ci gaba da tattaunawar tsakanin Malaman Jami’o’in da gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.