Isa ga babban shafi
Najeriya

Malaman Jami'o'in Najeriya sun janye yajin aiki

Kungiyar Malaman jami’oin Najeriya ASUU, ta sanar da dakatar da yajin aikin da ta shafe sama da watanni uku tana yi, inda ta bukaci malaman da su koma bakin aikin su daga yau Juma’a.

Wasu daliban Jami'a a Najeriya.
Wasu daliban Jami'a a Najeriya. The Guardian Nigeria
Talla

Shugaban kungiyar ta kasa Abiodun Ogunyemi ya bayyana dakatar da yajin aikin ne bayan kulla yarjejeniya guda 8 a taron da suka yi da wakilan gwamnati.

Yarjejeniyar tace bayan biyan naira biliyan 20 da gwamnati tayi a shekarar da ta gabata, za ta kuma sake bayar da naira biliyan 25 tsakanin watan Afrilu zuwa Mayu.

Ranar 5 ga watan Nuwamban da ya gabata, malaman jami’o’in Najeriyar suka soma yajin aiki, kan wasu bukatu da dama, wadanda ke kunshe cikin yarjejeniyar da suka cimma da gwamnati a shekarar 2009.

Wasu daga cikin bukatun sun hada da neman kara yawan kudaden gudanarwa da gwamnati ke baiwa jam’o’in tarayya, da kuma tabbatar da cewa ana baiwa jami’o’i mallakar jihohi isassun kudaden bunkasa su.

Wasu ‘yan Najeriya dai na zargin malaman jami’o’in da fifita kansu a maimakon yaran talakawa dangane da shiga yajin aikin, sai dai Dr Adamu Muhammad shugaban malaman a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, yace ba haka abin yake ba.

Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI Dr Adamu Muhammad, ya ce muddin kungiyar malaman jami’o’in bas u matsawa gwamnati kan inganta su ba, to fa nan gaba, jami’o’in na gwamnati za sui ya durkushewa, tamkar yadda makarantun Firamaren gwamnati a Najeriya suka fuskanci koma baya.

00:48

Dr Adamu Muhammad kan yajin aikin malaman jami'o'i

Bashir Ibrahim Idris

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.