Isa ga babban shafi
Najeriya

Babu wanda ya kai Obasanjo iya tafka magudin zabe - Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu, ya sake yin amfani da kakkausan harshe wajen sukar tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da jagoran jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, yayin yakin neman zaben 2019 a garin Maiduguri.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da jagoran jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, yayin yakin neman zaben 2019 a garin Maiduguri. Nigeria Presidency/Handout via Reuters
Talla

Tinubu wanda babban jigo ne a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, ya bayyana Obasanjo a matsayin wanda yafi kowa kwarewa wajen tafka magudi a zabukan kasar.

Tsohon gwamnan na Legas ya soki Obasanjo ne yayin yakin neman zaben shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya gudana a jihar ta Legas a wannan Asabar.

Tinubu ya ce tsohon shugaba Obasanjo ne ya jagoranci gudanar da zaben Najeriya mafi muni da aka tafka magudi a cikinsa a shekarar 2007, wanda Marigayi tsohon shugaban kasar Umar Musa ‘Yar Adua ya amince cewar zaben shekarar da ya kawo shi kan mulki, ba sahihi bane.

Alaka tsakanin Bola Tinubu da Obasanjo ta yi tsami ne tun daga shekarar 1999 zuwa 2007, lokacin da kowannensu ya rike mukaman shugabancin al’umma, wato na shugaban kasa da kuma gwamna.

A zamanin mulkin na su, Obasanjo da Tinubu sun sha banban akan wasu batutuwa da dama, daga ciki akwai rabawa jihohi da yankuna arzikin kasa, dadai wasu muhimman al’amuran da suka shafi tafiyar da gwamnatin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.