rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Najeriya Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

2019: Jam'iyyu sun yi barazanar kauracewa yarjejeniyar zaman lafiya

media
Akwatin kada kuri'a a Najeriya. guardian.ng

Jam’iyyu 42 a tarayyar Najeriya, sun yi barazanar kauracewa sa hannu kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya yayinda ya rage kwanaki kalilan a yi zaben shugaban kasar a ranar Asabar 16 ga watan Fabarairu.


Matsayar jam’iyyun na kunshe cikin sanawar da wakilansu suka fitar, da suka hada da shugaban jam’iyyar AA, Kenneth Udeze, shugaban PCP, Anthony Hamarttan da kuma Mashood Shittu na jam’iyyar ANP.

Gamayyar jam’iyyun sun ce muddin ana bukatar hadin kansu wajen kaucewa rikici yayin zaben, ta hanyar sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, tilas a cika wasu sharudda da suka gindaya.

Wasu daga cikin muhimman sharuddan sun hada da cewa tilas a kafe ko bayyana sakamakon kuri’ar kowane akwatin zabe kafin kaiwa hedikwatar hukumar INEC, sai kuma haramtawa jami’an tsaro kama jagororin ‘yan adawa da sunan tsare su yayin gudanar zabukan.

A ranar Laraba mai zuwa, 13 ga watan Fabarairu, ake sa ran ilahirin jam’iyyun Najeriya za su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, a karkashin jagorancin tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton.