rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Najeriya Najeriya APC

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Magoya bayan Amosun sun yi wa APC ihu a Abeokuta

media
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari yayin gangamin yakin neman zaben jam'iyyar APC. Premium Times

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta bayyana bacin ranta dangane da abin kunyar da ya faru wajen taron gangamin da ta yi a Abeokuta da ke Ogun, inda wasu da ake zargin magoya bayan Gwamnan Jihar, Ibikunle Amosun, suka yi ta ihu da jifan rumfar da manyan baki suke zaune.


Wannan ya tilastawa jami’an tsaro killace shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tabbatar da cewar babu abinda ya same shi.

Wannan matsala da APC ta samu a Ogun ta biyo bayan rarrabuwar kawunan da aka samu wajen tsayar da dan takarar gwamnan jihar, inda wanda Gwamna Ibikunle Amosun ke goyan baya ya fadi zaben fidda gwani, abinda ya sa shi komawa wata Jam’iyya domin yin takara.

Hakan ya haifar da dangantaka mai tsami tsakanin Gwamnan Jihar da shugabannin Jam’iyyar APC ta kasa.

Yayin da yake jawabi wajen taron na jiya, shugaban Jam’iyyar Adams Oshiomhole yayi ta fuskantar ihu daga masu goyan bayan Gwamnan.

Ihun nuna adawa da wasu mutane ke yiwa shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole a garin Abeokuta 12/02/2019 - Daga Bashir Ibrahim Idris Saurare

Wannan ya sa Gwamnan ya fto fili yana rokon masu jifar da su kwantar da hankalin su, kada su bashi kunya, inda yake cewa “ina rokon ku dan girman Allah, kada ku bani kunya, Babanmu yana nan.

Muryar gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun 12/02/2019 - Daga Bashir Ibrahim Idris Saurare

Daga karshe shugaban kasa Muhammad Buhari ya daga hannun dan takarar Gwamnan Jihar Dapo Abiodun, inda ya bukace su da su zabi Jam’iyyar APC ranar Asabar mai zuwa.

Muryar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari 12/02/2019 - Daga Nura Ado Suleiman Saurare