INEC ta dage zaben Najeriya zuwa makon gobe
Hukumar Zaben Najeriya ta sanar da dage zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisun da aka shirya gudanarwa yau asabar zuwa makon gobe, saboda wasu matsalolin da suka sha kan ta.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakub ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai cikin dare, inda ya bayyana fuskantar wasu matsalolin gudanar da ayyukan zaben, a matsayin wani bangare daga cikin dalilan da suka haddasa sauya ranar zaben zuwa gaba.
Farfesa Yakubu ya sanar da daukar matakin bayan taron da ya jagoranta tsakaninsa da masu ruwa da tsaki kan zaben na Najeriya, da kuma wasu wakilan masu sa ido kan zabukan na cikin gida na kasashen ketare, sai kuma manyan jami’an hukumar ta INEC.
A yanzu dai ya tabbata Zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisar Wakilai da Dattijan Najeriya zai gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabarairu, a maimakon 16 ga Fabarairu da aka tsara da farko.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu