Isa ga babban shafi
Najeriya

Na girgiza da matakin sauya ranakun zabe - Atiku

Dan takarar kujerar shugabancin Najeriya a karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar, ya bayyana kaduwarsa kan matakin dage zabukan kasar da aka shirya za a fara kada kuri’a cikinsa ranar 16 ga watan Fabarairu.

Dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya Atiku Abubakar.
Dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya Atiku Abubakar. REUTERS/Tife Owolabi
Talla

Atiku ya mayar da martani kan dage zabukan Najeriyar ne a babban birnin jihar adamawa, Yola.

Dan takarar na jam’iyyar PDP, ya ce abin damuwa ne matuka dangane da daukar matakin sauya ranakun gudanar da zabe, yayinda ya rage awanni kalilan a fara kada kuri’u, matakin da ya ce bai dace ba.

Dangane da batun muhimman kayayyakin zabukan kuwa, Atiku ya ce muddin za a basu cikakken tsaro, matsalar sauya ranakun zaben ragaggiya ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.