Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta bukaci shugaban INEC ya ajiye aikinsa

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, ta yi watsi da matakin hukumar zaben kasar INEC, na dage zaben shugaban kasa, ‘yan majalisar wakilai da kuma na majalisar dattijai, zuwa makon gobe.

Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya Uche Secondus.
Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya Uche Secondus. TWITTER/UcheSecondus
Talla

PDP ta ce rashin kammala shirin gudanar da zabukan karbar yadda aka tsara da INEC ta yi, wata makarkashiya ce da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tsara da gangan, domin ci gaba da rike madafun iko, duk cewa ta bayyana gwamnatinsa ta rasa goyon bayan ‘yan kasar.

Shugaban jam’iyyar PDP Prince Secondus ne ya bayyana zargin, a lokacinda da yake maida martani kai sanawar sauya ranakun zabukan na Najeriya, inda ya ce kamata yayi shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmud Yakubu ya ajiye aikinsa, saboda gazawar da tace ayyukan hukumar zaben ta yi a karkashinsa.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake dage manyan zabukan Najeriya ba, domin a shekarar 2015, a dage zabukan kasar da tsawon makwanni 6.

A waccan lokacin hukumar zaben ta danganta daukar matakin da matsalolin tsaro na hare-haren mayakan Boko Haram.

Sai dai APC wadda a waccan lokacin ke a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, tare da dan takararta na shugabancin kasa, kuma shugaba mai ci a yanzu, Muhammadu Buhari, sun zargi tsohon shugaba Goodluck Jonathan da yunkurin yin amfani da damar, wajen ci gaba da rike madafun iko.

A halin yanzu zaben shugaban kasa dana 'yan majalisun wakilai da dattijai zai gudana a ranar 23 ga watan Fabarairu, yayinda na gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jiha zai gudana ranar 9 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.