rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Maiduguri BOKO HARAM Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojin Najeriya sun hallaka manyan kwamandojin Boko Haram

media
Wasu sojin Najeriya yayin sintiri a garin Maiduguri, jihar Borno. REUTERS/Afolabi Sotunde

Dakarun rundunar sojin Najeriya sun hallaka wasu manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram uku a yankin Warawara da ke jihar Borno.


Dakarun Najeriyar sun samu nasarar ce bayan samamen da suka kaiwa maboyar kwamandojin na Boko Haram tare da mayakansu a ranar Asabar 16 ga watan Fabarairu.

Daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriya, Kanal Sagir Musa, wanda bai bayyana sunayen kwamandojin ba, ya ce yayin samamen, dakarun Najeriya sun kwace makamai da dama da suka kunshi, manyan bindigogi kirar AK 47 biyu, da kuma masu sarrafa kansu guda biyar, sai kuma babur.

Samamen dakarun Najeriyar ya zo ne sa’o’i bayan wani harin kunar bakin wake da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka kai a wani Masallaci da ke yankin Jidari Polo a garin Maiduguri.

Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu a harin, ciki harda mayaka uku da suka kai harin, wadanda biyu daga cikinsu, suka tarwatsa damarar bam din da ke jikinsu, yayinda wasu mutane 15 da ke gabatar da Sallar Asubahi da misalin karfe 5.40 suka jikkata.

Wadanda suka kai harin dai sun hada da ‘yan kunar bakin wake biyu da kuma dan bindiga daya.