rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Kaduna

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Miyetti Allah ta nemi 'ya'yanta su kaucewa daukar fansar harin Kajuru

media
A baya-bayan nan jihar Kaduna na yawan fuskantar rikici-rikicen kabilu wanda a lokuta da dama ke haddasa asarar rayuka, ciki har da hare-haren sari ka noke tsakanin mabanbantan kabilun jihar Reuters/Stringer

Kungiyar Fulani ta Miyattai Allah da ke Najeriya ta gargadi 'ya'yan ta su kaucewa daukar fansa kan kisan gillar da aka yi a karamar hukumar Kajuru da ke Jihar Kaduna, inda suka bukaci barin jami’an tsaro da gwamnati yin aikin da ya rataya a wuyan su.


Shugaban kungiyar na kasa Muhammad Kerewa, Ardon Zuru ya ce sun gamsu da matakan da gwamnati da jami’an tsaro ke dauka ya zuwa yanzu.

A cewarsa tsaron rayuka da dukiyoyinsu hakki ne da ya za rataya akan gwamnati da hukumomin tsaron da ke karkashinta, don haka za su bar doka ta yi aiki don hukunta masu hannu a kashe-kashen.

A baya-bayan nan jihar Kaduna na yawan fuskantar rikici-rikicen kabilu wanda  a lokuta da dama ke haddasa asarar rayuka, ciki har da hare-haren sari ka noke tsakanin mabanbantan kabilun jihar.

Ko a ranar 15 ga watan nan, makamancin hare-haren ya hallaka mutane 66 a karamar hukumar Kajuru galibi kuma fulani da ke zaune a jihar, wanda daga bisani adadin ya karu zuwa 130.

Tuni dai gwamnati ta yi umarnin daukar matakan da suka dace kan hare-haren, inda har rundunar 'yan sandan jihar ta sanar da kame mutane da dama da ke da hannu a harin.