rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Najeriya Najeriya Maiduguri BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Abubuwa masu kara sun fashe a Maiduguri

media
Abubuwan da suka fashe a sansanin ‘yan gudun hijira na Teachers Village. RFIHAUSA/Bilyaminu Yusuf

Mazauna wasu sassan garin Maidugri da ke jihar Borno, sun wayi gari da jin karar fashewar wasu abubuwa a wasu sassan garin, da suka hada da sansanin ‘yan gudun hijira na Teachers Village, Bolori da kuma Pompomari.


Sai dai wakilinmu Bilyaminu Yusuf, ya rawaito cewa ba a samu hasarar rayuka ba, kasancewa abubuwan da suka fashe basu rutsa da kowa ba.

Fashewar abubuwan, ya zo ne bayan da wasu gungun ‘yan bindiga da ake kyautata zaton cewa mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kai farmaki garin Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno a ranar Juma'a, sai dai wakilinmu dake garin na Maiduguri ya rawaito cewa sojoji sun yi gaggawar maida martani, inda suka yi nasarar korarsu.

Zuwa lokacin da muke wallafa wannan rahoton, wakilin na mu ya tabbatar da cewa, mutane da dama sun tsere daga gidajensu, zuwa Maiduguri, zalika babu karin bayani, kan adadin wadanda suka jikkata ko kuma suka rasa ransu.

Harin ya zo ne a dai dai lokacin da ‘yan Najeriya ke kada kuri’a a zabukan kasar na shugaban kasa da ‘yan majalisun dattijai da wakilai.