Isa ga babban shafi
Najeriya

Atiku ya doke Buhari a fadar shugaban kasa

Dan takarar jam’iyyar PDP mai adawa, Atiku Abubakar ya doke shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC a wasu rumfunan zabe da ke fadar shugaban kasa a  birnin Abuja.

Atiku Abubakar shi ne babban mai adawa da shugaba Muhammadu Buhari a zaben Najeriya
Atiku Abubakar shi ne babban mai adawa da shugaba Muhammadu Buhari a zaben Najeriya REUTERS/Tife Owolabi
Talla

Atiku ya samu kuri’u 525 rumfa mai lamba 022 da kuma kuri’u 505 a rumfa mai lamba 021, abin da a jumulce ya ba shi kuri’u 1,030.

Shugaba Buhari ya samu kuri’u 465 a rumfa mai lamba 022 da kuma kuri’u 548 a rumfa mai lamba 021, abin da ya ba shi jumullar kuri’u 1,013.

Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben na shugaban kasa da na 'yan majalisu da ya gudana a ranar Asabar, in da mutane sama da miliyan 72 suka kada kuri’unsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.