Isa ga babban shafi
Najeriya

Har yanzu ana cin zarafin matan da suka tserewa Boko Haram - Amnesty

Kungiyar Amnesty International ta zargi hukumomin Najeriya da rashin kyautatawa dubban matan da suka tsere daga yankunan da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Wasu daga cikin daruruwan matan da sojin Najeriya suka ceto daga hannun mayakan Boko Haram.
Wasu daga cikin daruruwan matan da sojin Najeriya suka ceto daga hannun mayakan Boko Haram. Reuters/Stringer
Talla

Zargin na kunshe ne cikin sanarwar da kungiyar ta fitar akan ranar mata ta duniya.

Rahoton Amnesty ya ce da dama daga cikin matan nan na shan wahala kafin samun abinci da sauran abubuwan more rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijirar da suke rayuwa a ciki, duk da takaita musu zirga-zirga.

Rashin samun kulawar da yakamata da takaita zirga-zirga na sa matan fuskantar cin zarafi daga jami’an hukumomin tsaro da ke ciki da wajen sansanonin.

Daraktan kungiyar Amnesty International, Osai Ojigho ya ce hana matan da suka fuskanci hare-haren boko haram hakkokin su ya sabawa ka’ida. Kuma a cewar Ojigho, jami’an tsaron sun dade suna cin zarafin mata a madadin abincin da suke basu, don su ciyar da kansu da kuma ‘ya’yan su.

Daraktan ya kara da cewa ko a shekarar da ta gabata sun fitar da rahoton da ke nuna yadda jami’an tsaro ke yi wa mata fyade da kuma barin su a cikin yinwa, sai dai gwamnati ta yi watsi da binciken.

Binciken na nuna cewa da dama daga cikin matan suna gab da fidda tsamanin samun adalci ganin yadda aka dade ana daukar musu alkawari ba tare da an cika ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.