Isa ga babban shafi
Najeriya - Kano

Kano: Yan Sanda sun kama Kwamishina da shugaban karamar hukuma

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Kano, ta tabbatar da kama kwamishinan kananan hukumomin jihar Kano Murtala Sule, da shugaban karamar hukumar Nasarawa Lamin Sani, saboda rudanin da suka haddasa wajen tattara sakamakon zaben Gwamna da na ‘Yan majalisunsa a karamar hukumar ta Nasarawa.

Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano Muhammad Wakili.
Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano Muhammad Wakili. Daily Trust
Talla

Wata sanarwa da kakakin Yan Sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya sawa hannu, ta ce manyan kusoshin gwamnatin na Kano sun kutsa kai cibiyar tattara sakamakon zaben na Gwamna ne tare da yunkurin lalata takardun da aka rattaba alkalumman sakamakon.

Shi kuwa mataimakin Gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna da shi me ya kutsa kai cikin cibiyar tattara sakamakon, wanda a baya aka bada rahoton cewa kama shi aka yi, rundunar Yan Sandan ta ce jami’anta sun tsare shi ne don janye shi daga inda rikicin ya so tashi.

Sanarwar ta kara da cewa tuni rundunar ‘Yan Sandan ta kaddamar da bincike kan lamarin, kuma duk wanda aka samu da lafi, zai gurfana a gaban Kuliya manta sabo.

Dangane da wadanda ke bikin murnar samun nasara a zaben na kujerar Gwamna kuwa, rundunar Yan Sandan ta shawarce su da su kyale hukumar zabe mai zaman kanta ta yi aikinta na bayyana wanda ya lashe zaben a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.