Kajuru: 'Yan bindiga sun raba mutane dubu 3 da muhallansu
Shugaban karamar hukumar Kajuru da ke Jihar Kaduna, Mista Cafra Caino, ya ce akalla mutane dubu 3000 sun rasa muhallansu, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga kan wasu yankuna da ke karamar hukumar.
Wallafawa ranar:
Yayin ganawa da manema labarai a wannan Juma’a, Caino, ya bayyana samun nasarar tsara hanyoyin magance matsalar tsaro a karamar hukumar ta Kajuru, bayan taron hadin gwiwa, tsakanin Kabilun Adara, Hausawa, da kuma Fulani da ke zaune a yankin.
Shugaban karamar hukumar ta Kajuru ya kuma koka kan yadda masu yada labaran karya ta hanyar kafofin sadarwa na zamani, suka kara hargitsa yanayin zaman dar-dar da mafi akasarin al’ummar yankin ke ciki.
Caino ya kara da bayyana rashin kyawun layukan sadarwar waya da hanyoyi, a matsayin manyan matsalolin da ke zama kalubale wajen tabbatar da tsaro a karamar hukumar ta Kajuru.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu