Isa ga babban shafi
Najeriya

Ban tsoma baki a zaben Gwamnan jihar Kano ba- Tinubu

Jagoran Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da rade-radin cewa, ya ziyarci jihar Kano domin tsoma baki a zaben Gwamna da za a sake gudanarwa a wasu yankuna na jihar.

Jagoran Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Bola Tinubu
Jagoran Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Bola Tinubu REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Tinubu ya ce, bai ziyaci Kano ba tun bayan fara gudanar da zabukan kasar.

Kazalika Jagoran na APC ya ce, hotonsa tare da Gwamna Abdullahi Ganduje da ake yadawa, tun shekarar 2018 suka dauka lokacin da Gwamnan ya kai wata ziyara a Lagos.

Tinubu ya ce, ire-iren wadannan rade-radin na cutar da demokradiyar da Najeriya ke fatan kafawa kuma illa ce ga ci gaban siyasar jihar Kano, yana mai cewa, shi cikakken magoyin bayan tsarin demokaradiya ne, a don haka ba zai aikata duk wani abu da zai gurgunta tsarin gudanar da zabe ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.