rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Najeriya Kano PDP APC

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

INEC ta bayyana Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben Kano

media
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje. Solacebase

Bayan shafe lokaci mai tsawo ana dakon sakamakon karashen zaben Kano, alkalumma daga hukumar zabe a jihar sun nuna cewa Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje ya lashe karashen zaben na jiya da kuri’u dubu 45,876, yayinda dan takarar PDP Injiniya Abba Kabir Yusuf ya samu kuri’u dubu 10,239.


Sakamakon karashen zaben Gwamnan da ya gudana a jiya daga Mazabar Gama a karamar hukumar Nasarawa ta kuma wata rumfar zaben daga karamar hukumar Kibya ne suka haifar da tsaikon kammala tattara kuri’un da aka sake kadawa a wasu yankunan kananan hukumomin jihar 28.

Yayin zaben ranar 9 ga watan Maris da muke ciki dai, alkalumman hukumar zaben a Kano sun nuna cewa PDP ke kan gaba da kuri’u miliyan 1 da dubu 14, da 474, APC na da dubu 987, da 819.

Amma bayan zaben jiya Asabar 23 ga watan Maris da muke ciki, alkalumman sun nuna APC ta samu kuri’u miliyan 1 da dubu 33 da 695, yayinda PDP ke da kuri’u miliyan 1 da dubu 24, da 713.

Tun a ranar Asabar Jam'iyyar adawa ta PDP, ta bukaci soke karashen zaben Gwamnan na Kano, inda ta zargi APC da yin amfani da karfin mulki da kuma 'yan daba wajen hana magoya bayanta kada kuri'a, kamar yadda shugaban Jam'iyyar ta PDP reshen jihar Kano Rabi'u Suleiman Bichi ya bayyana haka cikin sanarwar da ya rabawa manema labarai.

Rahotanni daga jihar Kanon sun tabbatar da cewa gungun ‘yan bangar siyasa dauke da makamai sun bayyana a mazabar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa, inda suka rika kai komo kan babbar hanyar yankin.

‘Yan bangar sun hana jami’an sa ‘ido da manema labarai gudanar da aikinsu a yankin, daga bisani kuma hargistin da ya tashi ya tilastawa mutane da dama tserewa, ciki har da wakilinmu da ya tsallake rijiya da baya.