rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Najeriya PDP APC

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ortom ya sake lashe zaben Gwamnan jihar Benue

media
Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom. Leadership Newspaper

Hukumar zaben Najeriya INEC ta bayyana Gwamnan Benue Samuel Ortom, a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Gwamnan Jihar a karo na biyu.


Benue na daga cikin jihohin da INEC ta bayyana zaben kujerun Gwamnoninsu a matsayin wanda bai kammala ba a ranar 9 ga watan Maris.

Bayan kammala tattara sakamakon karashen zaben da ya gudana a ranar Asabar 23 ga watan na Maris, INEC ta bayyana cewa, dan takarar PDP Gwamna Samuel Ortom ya samu kuri’u dubu 434,473, yayinda dan takarar jam’iyyar APC Emmanuel Jime ya samu kuri’u dubu 345,155.

Sakamakon ya nuna cewa Ortom ya lashe zaben jihar ta Benue da tazarar kuri’u dubu 89,318.