rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Najeriya PDP APC Sokoto

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tambuwal ya lashe zaben Sokoto

media
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal. Daily Post Nigeria

Dan takarar Jam’iyyar PDP a zaben kujerar Gwamnan Sokoto, da kuma ke kan Mulki, Aminu Waziri Tambuwal ya lashe zaben Gwmanan jihar karo na biyu.


Gwamnan jihar ta Sokoto ya lashe zaben ne da tazarar kuri’u 341.

Yayin bayyana sakamakon, Shugabar hukumar zaben Najeriya INEC a jihar ta Sokoto, Fatima Mukhtar, ta ce Tambuwal ya samu kuri’u dubu 512,002, yayinda dan takarar APC Ahmad Aliyu, ya samu kuri’u dubu 511,661.

A ranar 9 ga watan Maris da muke ciki, Tambuwal na kan gaba a zaben na Gwamna ne da kuri’u dubu489,558 yayinda Ahmad Aliyu na APC ke da kuri’u dubu 486,145, sai dai a waccan lokacin, an bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, sakamakon soke kuri’u dubu 75,403 da aka kada rumfunan zabe 136 da ke kananan hukumomin jihar ta Sokoto.