rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zaben Najeriya PDP APC Hakkin Dan Adam Kano

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya: Masu sa ido sun kadu da tashin hankali a zabukan karshen mako

media
Wasu daga cikin masu zabe a Kano, yayin shirin kada kuri'a a zaben da ya gabata. REUTERS/Goran Tomasevic

Masu sa ido kan zaben Najeriya sun bayyana matukar kaduwa dangane da irin tashin hankalin da suka gani a zaben da aka gudanar a Jihohin Kano, Sokoto, Bauchi da Benue a karshen mako.


Masu sa idon sun bayyana cewa an yi amfani da ‘yan bangar siyasa dauke da makamai, wajen tayar da hankulan masu kada kuri’a da nufin murkushe tasirin ‘yan adawa.

Kano, daya ce daga cikin jihohin da rahotanni suka tabbatar da cewa, an fuskanci tashin hankalin bayyanar ‘yan bangar siyasa dauke da makamai, musamman a mazabar Gama dake karamar hukumar Nasarawa.

Farfesa Jibrin Ibrahim na Cibiyar Bunkasa Dimokiradiya na daga cikin wadanda suka kalli zaben a Kano, ya kuma yi tsokaci kan abinda ya faru a tattaunawarsa da Bashir Ibrahim Idris.

Farfesa Jibril Ibrahim kan karashen zaben kujerar Gwamnan Kano 25/03/2019 - Daga Bashir Ibrahim Idris Saurare

‘Yan bangar dai sun hana manema labarai da jami’an sa ido kan karashen zaben kujerar Gwamnan jihar gudanar da aikinsu, kamar yadda wakilinmu ya rawaito.

Tuni dai jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon cewa Gwamnan Kano mai ci Abdullahi Umar ganduje ne ya lashe zaben jihar da tazarar kuri’u dubu 8, bayan samun jimillar kuri’u miliyan 1 da dubu 33 da 695, yayinda Injiniya Abba Kabiru Yusuf na PDP ke da kuri’u miliyan 1 da dubu 24, da 713.

Tun a ranar Asabar Jam'iyyar adawa ta PDP, ta bukaci soke karashen zaben Gwamnan na Kano, inda ta zargi APC da yin amfani da karfin mulki da kuma 'yan daba wajen hana magoya bayanta kada kuri'a, kamar yadda shugaban Jam'iyyar ta PDP reshen jihar Kano Rabi'u Suleiman Bichi ya bayyana haka cikin sanarwar da ya rabawa manema labarai.