Isa ga babban shafi
Najeriya

Rikici da sayen kuri'u sun yi tasiri a zaben Kano- EU

Masu sa ido na Kungiyar Tarayyar Turai sun ce, tashin hankali da sayen kuri’u da kuma firgita jama’a sun yi tasiri a yayin gudanar da karashen zaben Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Wasu daga cikin masu kada kuri'u a zaben jihar Kano
Wasu daga cikin masu kada kuri'u a zaben jihar Kano RFIHAUSA/Abubakar Isa Dandago
Talla

Kungiyar ta EU ta ce, ta damu matuka kan sakacin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC da hukumomin tsaro wajen magance tashin hankali da sauran matsalolin da aka samu a yayin gudanar da zaben na Kano.

A rahoton da ta fitar, EU ta ce, jami’anta sun shaida yadda wasu wakilai suka yi katsalandan da kuma sayen kuri’u a zaben na ranar 23 ga watan Maris.

Kungiyar ta ce, wasu ‘yan daba dauke da makamai su ne suka firgita jama’a tare da haifar da tarnaki wajen gudanar da zaben, lamarin da ya hana jami’anta da kuma ‘yan jaridu gudanar da ayyukansu cikin tsanaki.

Tuni Hukumar Zaben kasar, INEC ta bayyana Gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben domin ci gaba da jagorancin jihar a wa’adi na biyu.

A zaben da aka fara gudanarwa a ranar 9 ga watan Maris, dan takarar jam’iyyar PDP mai adawa, Abba Yusuf ya bai wa Ganduje tazaar kuri’u dubu 26, amma INEC ta ce, Gandujen ya sha gaban Yusuf bayan kammala gudanar da karashen zaben a ranar 23 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.