rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Maiduguri BOKO HARAM Chadi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dakarun MNJTF sun hallaka mayakan Boko Haram a Borno

media
Wasu dakarun Najeriya bayan korara mayakan Boko Haram daga garin Damasak. 18/3/2015. REUTERS/Emmanuel Braun

Dakarun sojin rundunar MNJTF, ta kasashen da ke fama da hare-haren Boko Haram mai hedikwata a birnin N’Djamena dake Chadi, tare da hadin gwiwar dakarun Najeriya a Borno, sun yi nasarar hallaka wasu mayakan Boko Haram 5, yayinda uku suka mika kansu.


Kakakin rundunar ta MNJTF Kanal Timothy Antigha, ya ce dakarun rundunar sun hallaka mayakan na Boko Haram ne Doron Naira da ke Borno, inda kuma uku suka mika kansu a Kamaru.

Kanal Antihga ya kara da cewa dakarun rundunar MNJTF sun yi nasarar kamawa tare da lalata wata mota dake yiwa mayakan na Boko Haram safarar man fetur da sauran kayayyakin da suke bukata, a tsakanin Damasak, Garunda da kuma Gazabure.

Zalika sojojin rundunar hadin gwiwar sun kuma kwance wasu bama-bamai uku da mayakan na Boko Haram suka binne a gefen hanya.