Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Koli ce za ta fayyace makomar APC a Zamfara - INEC

Hukumar Zaben Najeriya INEC, ta ce za ta saurari sakamakon hukuncin kotun kolin kasar, kafin daukar mataki na gaba, kan zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC a Zamfara.

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
Shugaban Hukumar Zaben Najeriya INEC, Farfesa Mahmood Yakubu. KOLA SULAIMON/AFP/Getty Images
Talla

INEC ta bayyana matsayinta ne, bayan matakin da ta dauka, na kin baiwa dan takarar APC Alhaji Muhktar Shehu takardar shaidar nasarar lashe zaben kujerar Gwamnan jihar.

A cewar hukumar zaben, ta dauki matakin ne saboda hukuncin kotun daukaka kara dake jihar Sokoto, na soke zaben fitar da gwanin jam’iyyar ta APC.

Tuni dai APC ta maida martani kan matakin na hukumar INEC, inda ta musanta cewa hukuncin kotun daukaka karar ya soke zaben fidda gwanin da ta yi, dan haka ta yi gaggauta mikawa dan takararta shaidarsa ta lashe zaben kujerar Gwamnan Zamfara.

Sai dai INEC ta hannun kwamishinanta na kasa kan wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye, ta sha alwashin bin doka da umarnin kotu kan takaddamar.

A cewar hukumar INEC ba ta da wani dan takara da ta fifita a jihar Zamfara, sai dai kawai ta damu ne da bin tsarin da doka ta shimfida, kafin tabbatar da nasarar dukkanin ‘yan takara a zabukan da suka gudana, ciki har da na jihar ta Zamfara.

A halin yanzu dai takkadama kan makomar APC a jihar Zamfara na gaban kotun Kolin Najeriya, wadda ake sa ran, nan da gajeren lokaci za ta yanke hukunci a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.